Cutuka guda 8 da aduwa take maganin su

Publish date: 2024-07-05

- Jerin cutuka guda takwas da itacen aduwa yake magani a jikin dan adam

- Ana amfani da ganyen, ko bawon, ko kuma dan wurin yin magunguna kala kala

Tun da can mutane sun dauki aduwa a matsayin sahihin magani, sai dai kuma kowacce kasa da yadda take amfani da ita da kuma yadda take sarrafa ta wurin magani, sannan kowacce kasa da irin maganin da take yi da ita.

A kasar mu ta Hausa, masu magungunan gargajiya sun cinye lokaci mai tsawon gaske suna amfani da ganye da 'ya'yan aduwa wurin maganin wasu cutuka.

Ga wasu daga cikin magungunan da aduwa take yi:

1. Ana amfani da garin ganyen aduwa da Ricinus Communis, a tafasa da ruwan zafi a dinga wanka dashi don magance kurajen fata, kazuwa, kunar wuta da kaikayin jiki.

2. Ana amfani da ganyen aduwa wurin magance cutar fitsarin jini.

3. Ana dafa bawon itacen aduwa a dinga shan ruwan domin maganin cutar kuturta.

4. Ana amfani da garin kwallon aduwa cokali daya a cikin kunun gero a dinga sha akan lokaci, yana maganin tsutsar ciki.

KU KARANTA: Tsugune bata kare ba a jihar Kano: An umarci Hakimai 44 na fadin jihar da su hallara a birnin Kano don gabatar da hawan sallah tare da Sarki Sanusi

5. Ana shan ruwan ganyen aduwa idan an dafa don maganin ciwon gudawa.

6. Ana amfani da garin kwallon aduwa wurin maganin cutar asma, idan aka daka kwallon a tafasa karamin cokali guda uku a dinga sha.

7. Ana yin kunun aduwa ana sha ga mai yawan amai da tashin zuciya. Sannan ana amfani da kunun wurin maganin hawan jini, idan ana sha.

8. Mace mai shayarwa zata iya amfani da garin ganyen aduwa a cikin kunun gero, domin tsaftace jininta da cikinta, sannan za ta samu isashen nono ga jaririnta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kW1ncnFlYrC2wNSkmGafpZmuboSMnZhmmZSqxKJ5zJqemqaZo3q0wY2hq6ak